Jigo a Jam'iyar PDP Ya Gargadi Abba Gida Gida Kar Ya Koma APC

Jigo a Jam'iyar PDP Ya Gargadi Abba Gida Gida Kar Ya Koma APC
 

Wani jigon jam'iyyar PDP, Rilwan Olanrewaju, ya bayyana Shugaban kasa Bola Tinubu a matsayin mutumin da ya dauki siyasa aiki, wanda ya fi mayar da hankali ga siyasa da zaben 2027 fiye da yadda yake jagoranci. 

A wata hira da jaridar Legit, Olanrewaju ya ce Tinubu ya yi watsi da kawo ci gaba a Najeriya. 
Jigon na PDP ya yi tsokacin ne yayin da yake martani ga kiran da shugaban jam'iyyar APC na kasa ya yi kan Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya dawo jam'iyyar mai mulki. 
Ana ta rade-radin cewa Gwamna Yusuf, wanda aka zaba karkashin inuwar jam'iyyar NNPP, yana kan hanyarsa ta komawa APC tun bayan sakamakon hukuncin Kotun Koli da ya dawo da shi kan kujerarsa bayan kotun kasa ta tsige shi. 
A martaninsa, Olanrewaju ya yi zargin cewa Tinubu ne ya kitsa kiran. Ya shawarci gwamnan Kano da ya dubi bayan 2027 sannan ya gina NNPP ta zama jam'iyyar adawa mai karfi. 
"Tinubu ya rigada ya watsar da batun kawo ci gaba a Najeriya. Ya mayar da hankali kan siyasa da 2027, wanda ba abu ne mai kyau ga talakawan Najeriya ba. 
"Akodayaushe kuskure ne kawo wanda ya dauki siyasa sana'a a matsayin shugaban kasa saboda babban abin da za a sanya gaba shine siyasa ba mulki ba. "Ina fatan Gwamna Abba zai iya duba bayan 2027 sannan ya mayar da hankali wajen sanya NNPP ta zama babbar jam'iyyar adawa a fadin kasar."