Jigo a jam'iyar PDP a  Sakkwato ya rasu

Jigo a jam'iyar PDP a  Sakkwato ya rasu
Allah Ya yiwa Alhaji Ibrahim Milgoma rasuwa a daren nan na Talata  a asibitin Zenith dake Abuja.
Ibrahim Milgoma jigo ne a jam'iyar PDP ta jihar Sakkwato wanda ya taba rike shugabancin jam'iyyar shekara hudu a matakin jiha.
Margayin sanannen dan siyasa ne dake da akida da ya yi gwagwarmaya don tabbatar da gaskiya a mulki.
Milgoma dan kasuwa ne da yake taimakon jama'a a lokacin rayuwarsa, ya rasu ya bar matan aure da 'ya'ya da jikoki.
Alhaji Yusuf Dingyadi ne ya sanar da rasuwar a kafarsa ta facebook.