Jigawa: Majalisar Dokoki Ta Dakatar da Shugabannin Kananan Hukumomi 3 

Jigawa: Majalisar Dokoki Ta Dakatar da Shugabannin Kananan Hukumomi 3 

 

Majalisar dokokin jihar Jigawa ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi uku, kan zargin fita wajen kasar ba tare da sun nemi izini daga bangaren zartarwa ko na dokokin jihar ba. 

Shugabannin kananan hukumomin da aka dakatar sun hada da Hon Mubarak Ahmed na karamar hukumar Birniwa, Hon Rufai Sunusi na karamar hukumar Gumel da Hon Umar Baffa na karamar hukumar Yankwashi. 
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, an yi zargin cewa yan siyasar sun lula kasar Rwanda ne. 
Majalisar ta dauki matakin ne, bayan shugaban kwamitin majalisar kan harkokin kananan hukumomi, Hon Aminu Zakari Tsubut, ya gabatar da kudirin don dakatar da ciyamomin da abun ya shafa. 
Ya bayyana cewa, kafin tafiyar tasu, majalisar ta bayar da wani umurni ga shugabannin kananan hukumomi a jihar na kada su yi tafiya zuwa ko'ina saboda shirya kasafin kudin jihar na 2024 da gabatar da shi gaban majalisa da gwamnan jihar, Malam Umar Namadi zai yi. 
Tsubut ya bayyana matakin da shugabanin kananan hukumomin suka dauka a matsayin rashin biyayya, nuna halin ko-in-kula ga babban nauyi dake kansu wanda ya kamata a bincika tare da hukunta su kamar yadda doka ta tanada.