Jigawa: Gwamna Namadi ya sanya hannu kan dokar kafa Hukumar Hisbah
Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya sanya hannu kan kudirin dokar kafa Hukumar Hisbah a matsayin hukuma ta doka domin tabbatar da kyawawan dabi’u da tsarin zamantakewa a jihar.
Wannan ya biyo bayan amincewar da Majalisar Dokokin jihar ta yi da kudirin a zaman ta na baya-bayan nan domin tallafawa ayyukan hukumar a fadin jihar.
A yayin sanya hannu kan dokar ranar Talata a gidan gwamnati dake Dutse, yayin taron majalisar zartarwa ta jihar, Gwamna Namadi ya bayyana cewa wannan mataki babban ci gaba ne da ya biyo bayan sama da watanni takwas na aikin hadin gwiwa tsakanin bangaren dokoki da gudanarwa.
"Yau mun sanya hannu kan dokar da ta kafa hukumar Hisbah a matsayin hukuma ta doka a jihar Jigawa," inji shi.
Ya ce ana sa ran hukumar za ta taka rawar gani wajen tabbatar da tarbiyya, adalci da kuma kawo zaman lafiya a jihar, tare da gargadin ma’aikatan Hisbah da su gudanar da aikinsu cikin tsoron Allah, adalci da gaskiya.
managarciya