Home Kiyon Lafiya Jerin Abinci Da Ke Janyo Hauhawar Sinadarain Uric Acid Da Ke Janyo...

Jerin Abinci Da Ke Janyo Hauhawar Sinadarain Uric Acid Da Ke Janyo Ciwon Gaɓoɓi

13
0

Nau’in ciwon gaɓoɓi na gawut, wato “Gout Arthritis” a turance, ciwo ne da ake alaƙanta shi da yawan cin jan nama.

To sai dai ga yadda lamarin yake 👇

A al’adance, jikin mutum na samar da sinadarin ‘purines’, yayin da jiki ya narka wannan sinadari zai haifar da wani sinadari da ake cewa ‘uric acid’. Sinadarin ‘uric acid’ zai narke ya bi jini sannan ƙoda ta tace shi zuwa cikin fitsari.

Amma duk lokacin da jiki ya samar da sinadarin ‘purines’ da yawa saboda yawan cin nau’in abinci/abinsha da ke ɗauke da sinadarin ‘purines’ ko kuma yayin da ƙoda ta gaza tace sinadarin ‘uric acid’ zuwa cikin fitsari, wannan zai haifar da taruwar sinadarin ‘uric acid’ a cikin jini fiye da ƙima.

Haka nan, taruwar sinadarin ‘uric acid’ a cikin jini fiye da ƙima zai sa ya riƙa duddunƙulewa har ya zama gishirin “urate”. Wannan gishiri na ‘urate’ shi ne ke taruwa a cikin gaɓoɓi ya haifar da ciwon gawut wanda ke haddasa matsanancin ciwo, kumburi da rirriƙewar gaɓɓai.

Bugu da ƙari, akwai nau’o’in abinci/abinsha daban-daban da muke ci yau da gobe waɗanda ke maƙare da sinadarin ‘purines’ ɗin. Kuma cin irin waɗannan abinci/abinsha fiye da ƙima na iya kawo hauhawar sinadarin ‘uric acid’ a cikin jini wanda kuma daga ƙarshe na iya haifar da ciwon gawut.

Daga cikin abinci/abinsha da ke ɗauke da sinadarin ‘purines’ akwai:

  1. Jan nama, kamar naman saniya, rago.
  2. Naman kayan ciki, kamar hanta, ƙoda, matsarmama.
  3. Naman ruwa, kamar jatan lande (shrimp), kifi sadin (sardines), ‘lobster’, ‘mussels’, ‘anchovies’
  4. Barasa/giya, abinci/abinsha da ke ɗauke da siga nau’in ‘fructose’ kamar lemukan roba, askirim (ice cream), alawar cakulet da sauransu.

Har wa yau, ganyayyaki kamar alayyahu (spinach) da shekan ɓera (asparagus) na ɗauke da sinadarin ‘purines’ sosai, sai dai bincike ya tabbatar da cewa sinadarin ‘purines’ da ke cikin alayyahu da shekan ɓera ba ya janyo hauhawar sinadarin ‘uric acid’ a cikin jini. Saboda haka, ba su shiga jerin abubuwan da mai ciwon gawut zai ƙaurace wa ba.

Yaushe za a fara ƙaurace wa waɗannan abinci/abinsha da aka lissafa?

Za a fara bayar da tazara ko ƙaurace wa cin irin waɗannan nau’o’in abinci/abinsha ne da zarar likita ya tabbatar cewa mutum na fama ciwon gawut.

Amma mutum zai iya ci gaba da cin waɗannan nau’o’in abinci/abinsha matuƙar ba a tabbatar yana da ciwon gawut ba ko kuma babu ƙorafin ciwo ko kumburin gaɓɓai a jikinsa. Sai dai, a har kullum mafi kyawun lamari shi ne tsaka-tsakinsa!

© Physiotherapy Hausa

Ku yi mana sharing domin wasu su amfana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here