Jam’iyyun adawa a Nijeriya na ƙara ƙaimi wajen tattaunawa kan yiwuwar tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya da zai fafata da Bola Tinubu a zaɓen 2027, in ji wani binciken jaridar Daily Trust.
Shugabannin jam’iyyun adawar sun gana da ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, a ranar Talata da dare a Abuja.
Wannan yunƙuri na daga cikin ƙoƙarin G-100, wata ƙungiyar ‘yan siyasa da ke neman haɗa jam’iyyun adawa kamar ADC, PDP, NDC, PRP, SDP da APM domin samar da matsaya ɗaya a zaɓen 2027.
Sai dai har yanzu akwai tambayoyi kan ko ‘yan takarar jam’iyyun da magoya bayansu za su amince da janyewa domin goyon bayan ɗan takara ɗaya tilo.






