Home Siyasa Jam’iyyun adawa na ƙoƙarin tsayar da ɗan takara guda dai zai kara...

Jam’iyyun adawa na ƙoƙarin tsayar da ɗan takara guda dai zai kara da Tinubu

15
0

Jam’iyyun adawa a Nijeriya na ƙara ƙaimi wajen tattaunawa kan yiwuwar tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda ɗaya da zai fafata da Bola Tinubu a zaɓen 2027, in ji wani binciken jaridar Daily Trust.

Shugabannin jam’iyyun adawar sun gana da ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, a ranar Talata da dare a Abuja.

Wannan yunƙuri na daga cikin ƙoƙarin G-100, wata ƙungiyar ‘yan siyasa da ke neman haɗa jam’iyyun adawa kamar ADC, PDP, NDC, PRP, SDP da APM domin samar da matsaya ɗaya a zaɓen 2027.

Sai dai har yanzu akwai tambayoyi kan ko ‘yan takarar jam’iyyun da magoya bayansu za su amince da janyewa domin goyon bayan ɗan takara ɗaya tilo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here