Jam'iyyar mu ba za ta yi maja da kowacce ba - Gwamnonin PDP
Gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP sun bayyana cewa ba za su yi haɗaka ko kawance da wata jam’iyya ta daban ba gabanin zaɓen 2027.
Gwamnonin sun bayyana matsayinsu ne a cikin wata sanarwa da suka fitar a ranar Litinin bayan wata ganawa da suka gudanar a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Tattaunawa kan yiwuwar haɗa kai don kalubalantar jam’iyyar APC na ƙara ɗaukar hankali yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa.
Haka kuma, ’yan adawa sun fara gudanar da wasu “taruka masu mahimmanci” a wannan fanni.
Ɗaya daga cikin manyan masu goyon bayan haɗakar jam’iyyu shi ne Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023.
Atiku Abubakar yana ci gaba da kira ga jam’iyyun adawa su haɗu kafin zaɓen 2027 domin su kwace mulki daga hannun gwamnatin APC ƙarƙashin shugabancin Bola Ahmed Tinubu.
“Domin la’akari da jita-jita da ke yawo a faɗin ƙasa game da yiwuwar haɗakar jam’iyyu, ƙungiyoyi da sauransu, taron ya yanke shawarar cewa PDP ba za ta shiga kowace irin haɗaka ko kawance ba,” in ji sanarwar.
Sai dai gwamnonin sun ce PDP na maraba da kowace jam’iyya, mutum ko ƙungiya da ke da niyyar shiga jam’iyyar domin kwace mulki daga APC a 2027.
managarciya