Jam'iyyar LP mai mulki ta gaza lashe ko kujera ɗaya a zaɓen ƙananan hukumomi na Abia 

Jam'iyyar LP mai mulki ta gaza lashe ko kujera ɗaya a zaɓen ƙananan hukumomi na Abia 

Jam'iyyar LP mai mulki ta gaza lashe ko kujera ɗaya a zaɓen ƙananan hukumomi na Abia 

Jam’iyyar Labour, LP, da ke mulkin jihar Abia ba ta lashe ko kujera daya ciyaman  a zaben kananan hukumomi da aka gudanar a jiya Asabar.

Lokacin da Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Abia (ABSIEC), Farfesa George Chima, ya sanar da sakamakon zaben a hedkwatar hukumar da ke Umuahia, babban birnin jihar, Jam’iyyar Zenith Labour Party (ZLP) ta lashe kujeru 15 na shugabancin kananan hukumomi, yayin da Young Progressives Party (YPP) ta lashe kujeru biyu.

Yayin sanar da sakamakon, Chima ya ce: “Mun gudanar da aikin da aka nada mu ranar 5 ga Satumba don aiwatarwa. Ba sauki bane, amma mun yi iyakar kokarinmu wajen wayar da kai game da zaben a fadin jihar.

Dole ne a lura cewa, a kwanan nan, wannan hukumar bata gudanar da zaben da fiye da jam'iyyu 12 suka shiga ba, wanda a wannan karon shi kansa alama ce mai kyau ga hukumar.”

Shugaban ABSIEC ya bayyana cewa an gudanar da zaben shugabanci da kansiloli a cikin dukkan kananan hukumomi 17 na jihar.

Ya bayyana zaben a matsayin “cikakken adalci da inganci”.

Ya ce zaben ya kasance alamar sadaukarwa, mayar da hankali da kwarewar hukumar wajen gudanar da ayyukanta.