Jam'iyar YPP Ta Musanta Yin Hadaka Da Kowace Jam'iya a Sakkwato

Jam'iyar YPP Ta Musanta Yin Hadaka Da Kowace Jam'iya a Sakkwato

Jam'iyar adawa ta YPP a jihar Sakkwato ta musanta maganar da ake yadawa a gari ta yi hadaka da jam'iyar APC domin samun nasara a zaben 2023.

Shugaban jam'iyar a jihar Sakkwato Honarabul Hussaini Usman ne ya karya ta jita-jitar a wata takarda da sakataren tsare-tsare a jiha Junaidu Muhammad ya sanyawa hannu aka rabawa manema labarai, ya ce "wannan ba gaskiya ba ne jam'iyar YPP tana nan zamanta jam'iya a Sakkwato ba ta yi hadaka da kowace jam'iya ba, kawai dai wasu daidaiku ne daga cikinta suka koma APC kamar yadda aka saba a cikin siyasa ana canja sheka.

"Saboda haka jam'iyar YPP tana kira ga magoya bayanta su yi watsi da wannan jita-jitar ba gaskiya ba ne," a cewar bayanin.