Jam'iyar APC na takura wa 'yan adawa – Atiku
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi jam'iyyar APC mai mulki da takura wa ƴan adawa a Nijeriya.
Ya yi wannan martanin ne bayan kalaman da Kakakin Yada Labarai na APC, Felix Morka, ya yi kan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaɓen da ya gabata, Peter Obi.
A jiya Litinin, Obi ya yi zargin cewa saƙon sabuwar shekararsa game da halin da ƙasar ke ciki karkashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jawo barazana ga rayuwarsa da iyalinsa.
Ya bayyana wannan ne bayan da Morka, a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise , ya ce: “Peter Obi ya karya doka sau da yawa, kuma duk abin da ya same shi yana da alaka da abubuwan da ya aikata.”
Da ya ke mayar da martani, Atiku a wani saƙo da ya wallafa ta X a yau Talata, ya ce wannan lamari “yana nuna wata hanyar da ba ta dace ba da wannan gwamnatin ke amfani da ita wajen tunkarar yan adawa.”
managarciya