Jami'an hukumar Immigration sun kama mai safarar mutane tare da ceto mata 2 a Sakkwato

Jami'an hukumar Immigration sun kama mai safarar mutane tare da ceto mata 2 a Sakkwato

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa, NIS, reshen bodar Illela, Jihar Sakkwato, ta kama wani da ake zargi da safarar mutane, Sirajo Illela, tare da kubutar da wasu mata biyu da ke kan hanyar su zuwa kasar Libya.

Kwanturolan rundunar, Tony Akuneme ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, Abdullahi Mohammed ya fitar a yau Laraba a Abuja.

Akuneme ya ce an kama mutumin ne a gidan sa da ke unguwar Yar Kara, karamar hukumar Illela a yau Laraba din.

Ya ce an samu mata biyun masu sunaye  Maryam Akinosi mai shekara 40 ‘yar jihar Ogun da kuma Olatunde Abidemi mai shekaru 26 daga jihar Oyo, inda ya ce za su yi tafiyar ne ba tare da wasu sahihan takardu da ake bukata ba.

Ya kuma ce binciken farko ya nuna cewa suna kan hanyarsu ne ta zuwa kasar Libiya.