Iskan Damina Ya Yi Sanadiyar Rugujewar Gidaje Sama Da 500 a Kebbi

Iskan Damina Ya Yi Sanadiyar Rugujewar Gidaje Sama Da 500 a Kebbi
Daga Abbakar Aleeyu Anache
Mahaukaciyar guguwa hadi da ruwan sama ta biyu ta afka wa al'ummar Zuru inda ta yakice rufin gine-gine da kada bishiyoyi ta kuma haddasa mummunan ta'adi
Al'ummar mafarautar Zuru da ke jihar Kebbi na bukatar agajin gaggawa kan wata mahaukaciyar guguwa da ta yi sanadiyar ruguje gidaje sama da 500.
Wata mahaukaciyar guguwa da ruwan sama mai karfin gaske da aka yi a ranar Alhamis ta yakice rufin gine-gine da haddasa hasarar dukiyoyi a karamar hukumar Zuru.
Jama'ar Zuru da ke jihar Kebbi a Arewacin Najeriya sun ce wata iska mai karfin gaske da ta afku a daren jiya Alhamis ta yi sanadiyar ruguje gidaje tare da yakice rufin gine-gine.
Mahaukaciyar guguwar ta yi sanadiyar faduwar bishiyoyi da rufin gidaje na kwarewa gilsan tagogi na ta fashewa a daren jiya.