Home Labarai INEC ta goge rajistar masu zaɓe Miliyan 1.6

INEC ta goge rajistar masu zaɓe Miliyan 1.6

19
0

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta cire rajistar masu zaɓe 1,608,660 da aka gano ba su da cika ka’idoji ba, bayan kammala tantance bayanan rajistar zaɓe ta 2025/2026.

Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan ranar Litinin yayin ganawa da manema labarai kan sakamakon aikin tantance rajistar.

Ya ce hukumar ta kuma cire bayanan mutane 1,749 da aka tabbatar sun rasu, bayan gano wasu ƙarin sunaye a yayin tantancewar.

A cewarsa, hukumar ta karɓi bayanan rajista 11,088,238 daga matakai uku na aikin rajistar masu zaɓen.

Ya ƙara da cewa an gano jami’an rajistar zaɓe 54 daga jihohi 10 da ake zargin suna da hannu wajen wasu kura-kurai, waɗanda za su iya fuskantar matakin ladabtarwa ko gurfanarwa a kotu.

INEC ta ce za ta fitar da sahihiyar rajistar masu zaɓe da aka gyara a ranar 16 ga Disamba, 2026.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here