INEC Ta Dakatar Da Kwamishinan Zaben Sakkwato  Kwana 4 Kafin Zaben Gwamna

INEC Ta Dakatar Da Kwamishinan Zaben Sakkwato  Kwana 4 Kafin Zaben Gwamna

 

Hukumar zabe ta kasa ta umarci kwamishinan zabe dake kula da ofishinta a jihar Sakkwato Dakta Nura Ali ya janye kansa daga gudanar da aiyukkanta a jihar, in da ta maye gurbisa da Sakatariyar mulki ta hukumar Hauwa Aliyu Kangiwa anan take.

 
Hakan na ƙunshe ne a wata wasiƙa mai ɗauke da sa hannun Sakataren INEC, Rose Orlaran-Anthony, zuwa ga REC ɗin da Sakataren hukumar na jihar. 
Wasiƙar ta umarci Dakta Ali ya tattara ya bar ofishin hukumar INEC dake jihar Sakkwato, Arewa maso yammacin Najeriya, har sai baba ta gani.
Duk da wasiƙar ba ta ambaci dalilin ɗaukar mataki kan REC ɗin ba, amma wata majiya a INEC ta shaida wa Daily Trust cewa yana da alaƙa da abinda wasu ma'ikatan karkashin Ali suka yi a zaben da ya gabata. 
Managarciya ta tattaro zaben da ya gudana a Sakkwato wanda cike yake da matsaloli da jinkiri, idan aka kare  na shugaban kasa wanda PDP ta samu nasara, sauran an ce ba su kammalu ba har da na Sanatoci uku da 'yan majalisar tarayya 11.
"Kun san an samu jinkiri da dama a zaben da ya gabata, rashin zuwan kayan zaɓe rumfunan kaɗa kuri'a da wuri da rashin baiwa ma'aikatan wucin gadi horo mai kyau da rashin jami'an tsaro a rumfunan zabe." 
Wannan ne karo na farko da Nura Ali ya jagoranci zaɓe tun bayan naɗa shi a matsayin kwamishina a shekarar da ta gabata.