INA HUJJAR TAKE: Labari Mai Sosa Zuciya Fita Ta Shidda

INA HUJJAR TAKE: Labari Mai Sosa Zuciya Fita Ta Shidda

  Page 6

 

 

Inna Kande dai na waje batasan wainar da Lantai ke toyawa ba.

 

Lantai ta sake dubawa ko ina ba littafi ba hankalinta ya tashi haiƙan, ta rasa abin da ke mata daɗi ta fice daga gidan batare data ko kalli inda Inna Kande take zaune ba.

 

Inna Kande ta bi bayanta da kallo ta ce, "Umma ta gaida ashsha yarinya sai neman maganar tsiya."

 

Lantai na fita ta sake bin hanyar data biyo lokacin data dawo daga makarantar, sai dai bata ga ko mai irin littafin ba, har ta isa makarantar ta iske ba kowa an jima da tashi.

 

Ta zauna ƙofar office ɗin su Malam Muntasir ta dinga kuka tana cewa "Wayyo abuna, ni sai naga abina wallahi bazan yadda ba."

Taci kukanta mai yawa har fuskarta ta fara kumbura ta miƙe ta sake bin hanyar ta koma gida, har idan taga tarin ƙasa sai ta yamutsa wai ko littafinta na ciki.

 

Tana isa gidan ta sake wucewa banɗakin ta duba bata dai ganshi ba ,sai ranta ya fara bata cikin biyu za a samu ɗaya inda yake ko dai cikin shaddar gidan ko cikin rijiyar gidan dole a sameshi waje guda.

 

Ita kuwa Inna Kande ta lura yau Lantai ba zata tsinana mata komi ba a gidan sai ta miƙe ta kama aikinta na girkin abinci tana cikin aikinne ta ci karo da fanken nan guda da Lantai ta ɗauko gun Musa sai tayi tunanin ko shi Lantai ke nema duk ta ruɗe haka? Tasan Lantai da son fanke don haka ta ɗauki fanken ta kira Lantai ɗin "Lantai zo ga abin da kike ta nema."

 

Lantai ta kwaso da gudu ta shigo ɗakin fuska ɗauke da murmushi.

 

Inna Kande ta miƙa mata fanken itama da fara'a kwance a fuskarta.

Lantai tai sototo tana kallon fanken ta amsa ta zauna ta miƙe ƙafafuwanta ta gutsira ta fashe da kuka sosai har waje ana jinta.

 

"Wayyo ni Lantai na mutu na mutu ni Lantai ."

 

Inna Kande ta fara gajiya da koke-koken Lantai ta zaro zaborinta (Tsintsiyar kwakwa) ta rufe Lantai da duka taita tsula mata ita.

 

Da gudu Lantai tabar gidan tana kuka.

 

"Yarinya kin isheni da kuka don sakarci to yanzu ai sai kiyi na gaske ko ? Nasha gaya maki kukan banza kashe mutane yake na kusa da mutum kin ƙi bari."

 

Lantai ta koma ƙofar gidansu ta kwanta ƙasa taita kuka tana Inna Kande ta kasheta ga abinta ya ɓace ita ba zata yadda ba.

 

Mutanen layin tun basu damu da ita ba har suka fara mata magana tai haƙuri ta bar kukan ta koma gida amma kamar ƙara tunzura ta suke .

 

Tai buɗu-buɗu da ita amma ko a jikinta kukanta take kawai tana abinta ya ɓace ba zata yadda ba.

 

Sauri yake kada ya rasa motar da zata kai shi garinsu don haka ko tsayawa gaisawa da iyayen yara bai yi sai dai ya ɗaga masu hannu ya wuce.

 

Tun daga nesa ya ɗauki muryarta, sai abin ya ba shi mamaki taya Nuratu zata yi kuka cikin layinsu to ita da wa ?

Ina Inna Kande take aka bugi ƴar gaban goshinta ?

 

Lokacin daya isa gun ya hango Inna Kande da kwanon abinci tana ajema Nuratun tana cewa

 

"Ni kukanki bai damuna ki yi ta abinki amma ki tabbatar da kinci abincin nan sai kinfi jin daɗin kukanma."

 

Nuratu dai bata kulaba sai ihun ta bani ta lalace abinta ya ɓace take.

 

"Inna lafiya ke da tawajenki kuma yau ? Cewar Malam Muntasir kenan dake tsaye kansu .

 

Inna Kande ta ba shi labarin abin da yaru duka .

 

Lantai kuwa kallon jakar dake rataye a kafaɗarsa take ranta na bata littafin na ciki.

 

"Sake saka ihu tayi tana abata abinta ai ya zama nata ba zata yadda ba fa.

 

Murmushi yayi yana jinjina lamarin yarinyar domin tayi abin duka an daketa abu ya zama jangwam.

 

Dubanta yayi "Nuratu mu je daga ciki in ji wane  abinki ne kike nema ?

Ba kunya haka ta miƙa hannu ta ɗauki kwanon abincin har ta shiga zaurensu ta juyo da gudu ta ce , "Malam bari na je gun Musa Na zo." Ta shige zaurensu Musa .

 

Inna Kande ta ce "yaron daya sa ya faɗa rijiya zata kaima abincin ai Lantai duk da shirmen akwai sanin ya kamata."sai yaƙe baki take Lantai zatai abin kirki.

 

Sai kawai ya ji yana son ganin yaron da ake maganar zata kaima abincin.

 

Yace "Inna ko za ki rakani na dubo shi  ?

 

Inna Kande ta shige tana cewa biyoni .

Da hanzarinta ta isa ɗakin da Musa yake, ga kwano  ajiye gefenshi ga alama bai san an kawo ba.

Ta buɗe kwanon ta ci karo da Alala taji mai da yaji .

 

Ta kalli fagen tsakin da ke hannunta ta ce, "Yo wai kai shike nan yau kayan daɗi za ai ta saimaka ?

To bari muyi musayar wannan tunda anjima ban san me za a saima ba.

Kai wannan shiga rijiya ai gaba ta kaika, ji irin uban fanken dana iske ɗazun kana ci, yanzu kuma ji uwar alalenka tasha mai da yaji, to ai masu ciwo sun fi son abin da ke da ruwa-ruwa don haka faten tsakinnan ya dace da kai Musa.

 

Ta aje kwanon fatenta ta ɗauki kwanon alalen.

 

Musa cikin barci ya ji maganarta don haka ya buɗe ido don ganin dame ta zo yanzu kuma ?

 

Ta dube shi fuska duk jirwayen hawaye sun bushe ta ce, "Sannu Musa na rantse da Allah kai abin murna ne ma gunka ai, don yadda ake kulawa da kai kasan da ba mai maka haka."

 

"Lantai me ya saki kuka ne har fuskarki ta nuna ?

 

Kallonshi tayi baƙin ciki ya bayyana a fuskarta ta ce, "Musa sabon littafina ya ɓace na rantse da Allah akan littafin nan sai na yamutsa ƙauyen nan, don yanzu haka wannan alalen zan gama ci na nufi neman littafina domin akan littafin nan ba zan ɗagawa kowa ba a ƙauyen nan ciki hada su Dagaci da Mai garin duk sai sun san anmun ba daidai ba a wannan ƙauyen."

 

Zaune ya tashi yasan halin Lantai sarai yarinya ce mai kafiya da nacin duk abin da ta furta amma wannan karon yasan ba zata iya aikata abin da ta ce ba, tunda ta sako su mai gari a lamarin.

 

"Lantai ke ko wane littafine wannan mai daraja gunku ko na shiga makarantar gaba da primary ɗin ne ?

 

Yamutsa fuska tayi, "Allah Musa da abin takaici kake, ni da kake gani nan duk malaman makarantarmu babu wanda nake shakka ko shayi sai Malam Muntasir shima fa kaɗan, don sau tari wayau nake masa ma idan nayi ma shi laifi."

Dariya Musa ya saka "kice dai babu wanda kike shakka kawai Lantai."

 

"A'a shi kam ina shakkarsa domin bai dukana amma daya ke yasan yadda ake mugunta sai yayi ta samu aikin da zan gaji don haka nake shakarshi ai."

 

"To yanzu kenan hada shi cikin waɗanda za su bani a ƙauyen nan tunda ciki yake ko ?

 

Ta kwashe da dariya ta ce, "Zan baka labarin abin da nake masa ai yafi kowa banuwa ma."

 

Suna magana tana cin alalen ta cinye tas ta miƙe tsaye da zummar tafiya taga Malam Muntasir tsaye jikin ƙofar ɗakin yana ta kallonta.

 

Musa ta kalla ta sake kallon Malam Muntasir ɗin.

 

"Tab na rantse da Allah duk abin da na gayama Musa ƙarya nayi maka, kai dai Allah ya baka lafiya kawai ai kana jin jiki."

 

Ba Musa ba hatta shi Malam Muntasir ɗin sai da dariya taso ƙwace ma shi, dakewa kawai yayi.

 

Ganin Musa na murmushi ta ce, "Kayi abin da babu kyau ai domin sai ka min faɗa ai kace babu kyau ƙarya amma sai ka biye min." Ta zabga ma shi harara.

Yanzu me zan gayama malamin islamiyyarmu akan wannan baƙar ƙarya dana zabga ? Ko da yake daɗin alalen ne yasa na dinga sakin layi ban ankara ba, sauƙi na ɗaya ban gulmar kowa ba ko Musa ? Ta kalli Musa tana langwabe kai.

 

Musa dai sai murmushi yake mata, don tunda ta fara zuba Malamin nasu ke tsaye bayanta, yaso yayi mata magana ko shi sai Malamin ya hanashi da hannu.

 

Lantai tai tsaye firi-firi sai raba ido take ga Malam Muntasir ya tare ƙofar balle ta ruga, ga shi ko alamar fara'a babu akan fuskarshi sai ta sake natsuwa ta dubi Musa ta ce,

"Ka tuna labarin dana baka na Malamin dake matuƙar sona yana taimakona a makaranta ? Ta nuna Malam Muntasir ta ce to ka ganshi nan don Allah tayani gode masa ai har  Inna Kande sai nasa ta gode ma shi yau."

Hanya ya bata ta kuwa kwasa da gudu saura kaɗan data bugeshi ta fice ba ko waige.

 

Girgiza kanshi yayi ya shiga gun Musan.

 

Tana kowama gidan ta shige banɗaki ta yi tsit yau fa ta kira ruwa da yawa, amma hakan ba zai hana ta binciki jakar Malam Muntasir ba, ƙilama akwai littafin banda wancan.

 

Tuna hakan yasa ta fito daga banɗakin kai tsaye ta shige ɗakin gun Inna Kande ta dubeta ta ce, " Inna Kande kin san wani abu kuwa ? Malam Muntasir fa jakarsa da kike gani akwai wani goro wanda yake kaima Babanshi yace goron daga ƙasar waje yake wai idan mutum ya ci goron akwai wasu sirrika da masu cin goro ne kawai suka san su, yace kuma wai goron na ƙara ƙarfi da lafiyar jiki idan ka ɓalla sau guda yini yake a bakinka bai lalace ba."

 

Kowa yasan yadda ko da yaushe Inna Kande ke aiken Lantai siyen goro duk safiya da yamma don Allah yayi mata cin goro na gasken-gaske.

Ai sai ta fara haɗe miyau daman yau tashin hankalin da suke ciki ne ya hanata aiken Lantai siyen goron yanzu tana jin Lantai ta ambaci goron sai ta kama haɗiyar yawu (Miyau)

Lantai tai dariyar samun nasara ta ce, Ba don kada ki tona ni ba, ai da na ɗauko maki tunda ya zo da jakar."

 

Inna Kande ta ce , "Ai ko baki duba na riƙe shi ya sammun ko kaɗan ne."

 

Lantai ta gimtse fuska ta ce, "Ba fa zai baki ba, tunda bai son kowa yasan da shi nima sa'ar yana magana nayi har naji."

 

Cikin lokaci kaɗan Lantai ta tsarama Inna Kande yadda za su yi jakar Malam Muntasir ta je hannunta don ta ɗauki goron.

 

Musa ya dubi Malam Muntasir yayi murmushi yace, "Sannu da ƙokari tabbas ina jinjina maka sosai yadda kake tsaye kan Lantai, sai dai akwai matsala fa."

 

Malam Muntasir ya dubeshi da alamar tambaya.

Cikin damuwa Musa ya gaya ma shi abin da Lantai ta ce akan littafin daya faɗi nata.

Dariya yayi, "Yanzu Musa hada kai a masu tsoron shirmen Nuratu ? To littafin na wajena kuma nawa ne ta ɗauke daman tana gudu ta yadashi ɗaya daga ɗalibai na ya tsinta ya kawo min."

 

Musa yasha mamaki kenan daman wajenshi take ɗaukar littafan ?

 

Malam Muntasir yayi masa ya jiki ya koma gidansu Lantai yasan dole ta binciki jakar amma jin abin da ta ce yasa ya fasa aje mata jakar ya yi sallama da Inna Kande ya fito.

 

Yana jin Nuratu na cewa, "Yau na shiga uku indai ban ɗauki jakar nan ba."

 

Har waje Nuratu na biye da shi, yana kula da yadda take kawowa jakar warta sai ta fasa.

 

Kallonsa tayi "Malam don Allah ina zaka haka da ƙatuwar jaka kawo na riƙe ma ita."

 

"Nuratu kenan mata basu ɗaukar abu mai nauyi kinga ba zan baki wannan ƙatuwar jakar ba."

 

Lantai ta riga tasa a ranta yau duk yadda za ai sai jakar ta je gunta, shi kuma malam Muntasir yana ankare don haka ya hanata jakar yace ta wuce gida haka nan shima da garinsu za shi amma yanzu sai gobe dare yayi.

 

Da murna fal ranta ta dubeshi "Don darajar Allah sai gobe zaka tafi garin naku ?

 

Tabbatar mata yayi ta kuwa fasa ihu ta kwasa da gudu ta sha wata kwana abinta.

 

Da ido ya bita yasan wani abin za tai kenan.

Ita kuwa Lantai bata sauka ko ina ba sai ƙauyensu Barbushe kai tsaye dabarsu ta isa...

 

To ko me zata yi a dabar su Barbushe ?

 

 

To Ummu Affan ga wannan koyi maleji don jin daɗin comments ɗin da kika mun jiya.

 

 

Haupha