Ina ba 'yan mata da ke sha'awar shiga harkar fim shawara da kada su shiga - Hadiza Gabon

Ina ba 'yan mata da ke sha'awar shiga harkar fim shawara da kada su shiga - Hadiza Gabon

Hadiza Gabon a cikin shirin da take gayyatar fitattu a bangarori daban-daban na Ganin Room Talk Show, ta ce idan mutum ya shiga fim, zai yi suna a duniya da hakan ke sanya bakin mutane ya yi masa yawa na ko da bai yi abu ba, za a ce ya yi.
Jarumar masana'antar ta Kannywood ta ce akwai ma mutane da yawa da ke yi wa 'yan fim kallon 'yan marasa tarbiyya. 
Ta ce rashin amfanin yin fim ga mace yafi amfanin yawa don haka duk wadda ta nemi shawarar ta, tana son shiga fim takan faɗa mata koma gida ki yi karatu ko ki yi aure amma in ta matsa kan sai ta yi fim takan yi mata fatan alheri.
Wadannan da ma karin wasu hujjoji ne Hadiza Aliyu Gabon ta bayar game da shawararta ga mata masu tasowa da ke son shiga harkar fim a wannan lokacin.