ImpeachBuhariNow: Ma'abota Facebook Na Goyon Bayan Tsige Shugaba Buhari

ImpeachBuhariNow: Ma'abota Facebook Na Goyon Bayan Tsige Shugaba Buhari

 

A ranar Alhamis, 4 ga watan Agusta 2022, Lauyan nan mai tashe a Kano, Abba Hikima Esq. ya nuna cikakkiyar goyon bayansa na tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari. 

“Ni, Abba Hikima Esq, namiji, baligi, Musulmi, dan Nigeria, yaren Hausa, ina goyon bayan matakin Majalisar tarayya na tumbuke Shugaba Buhari a watan Satumba mai zuwa saboda gazawar sa wajen tsare rayukan mu. #ImpeachBuhariNow 
Da yake karin bayani, Hikima ya jero amfanin majalisa ta tsige shugaban kasar, yace hakan zai zama misali ga shugabannin da za ayi nan gaba a Najeriya. 
Lauyan yace hakan zai nuna riƙar dimukradiyya, sannan zai ƙara ƙarfafa gwiwar ‘yan majalisa, tare da sa ran samun saukin rashin tsaro da ya ta’azzara. 
Bayan nan aka ji Ibrahim Waziri yana cewa ya yi na’am da kiran Sanatocin. Kwararren marubucin yace tun tuni ya so a rika zanga-zanga domin nuna fushi. 
Ni, Abdulaziz T. Bako, MBBS, MPH, PhD, namiji, baligi, Musulmi, dan Nigeria, yaren Hausa, ina goyon bayan matakin Majalisar Tarayya na tumbuke Shugaban kasa Manjo Janar Buhari a watan Satumba mai zuwa saboda gazawar sa wajen tsare rayukan mu. #ImpeachBuhariNow