Illoli Da Amfanin Ganyen SHUWAKA Ga Lafiyar Mutane

SIRRIN MU MATA GROUP
Mutane da dama kan yi amfani da shuwaka ne kawai a matsayin ganyen miya, amma in an yi amfani da ganyen yadda ya kamata, akwai magunguna da dama a jikinsa.
1.Ciwon Hanta. Ganyen shuwaka magani ne mai kyau na ciwon hanta ana amfani da shi kamar haka:
2.A Markaɗa namijin goro guda 20 har ya zama gari sannan a zuba cikin ruwan lemon tsami (Lime juice) a kawo kwalba daya na zuma mai kyau a haɗa su duka a waje ɗaya a gauraya.
3. Markaɗe ganyen shuwaka guda 40 a zuba cikin ruwa mai kyau da ya kai lita 4 a rinƙa shan kofi guda sau 3 a rana har na tsawon watanni biyu. Wannan yana magani sosai na ciwon hanta, in ruwan ya dade ana iya sake wani sabon jiƙon.
4. Zazzaɓi: A tafasa busasshen ganyen shuwaka (gram 10) a samo gram 25 na busasshen garin TUMARIC a dafa a cikin ruwa kofi daya har sai ya tafasa. Tun da ɗuminsa sai a sanya zuma cokali ɗaya, daga nan bayan ya huce sai a sha sau uku a rana. Yana warkar da zazzaɓi sosai.
5. Sanƙara (Cancer) ƙari (Kulum Da Ke Fita A Jiki) Shan ruwan da aka tatse daga ganyen shuwaka yana taimakawa wajen rage girman ƙari da jinkirtar da girman ƙwayoyin cutar sanƙara.
6.Hawan Jini: Ruwan ganyen shuwaka na taimakawa wajen rage yawan gishiri a jikin mutum domin yana dauke da sinadarin ‘potosium’ mai yawa, hakan kuma na kawo saukin hawan jini.
7.Ciwon Suga: Yawan shan ruwan ganyen shuwaka a ƙa'idance yana saukar da yawan su da ke cikin jini don haka na rage karfin cutar sugar.
8.Kaikayin JIKI: A samu gram daya na ganyen shuwaka da gram daya na garin citta a markade har sai ya zama gari sai a sanya a cikin ruwa mai kyau a gauraya a rinka sha sau uku a rana. Yana maganin kaikayin jiki sosai.
9.Maleriya: A samo ganyen shuwaka cikin tafin hannu a dafa a ruwa kofi hudu har sai ya ƙone ruwan ya zamo kamar saura kofi biyu sai a rinka sha sau uku a rana.
10.Ciwon Afendis(Appendicitis): A samo busasshen ganyen shuwaka gram 30 da ruwa 400ml da zuma mai kyau cikin babban cokali sai a dafa har sai ya kone ruwan ya zamo rabi sai kuma a sauke a kara cokali guda na zuma kuma in ya yi sanyi sai a rinka sha sau uku a rana a kai a kai.
11.Zazzabin Shawara (Typhoid): Haka kuma shuwaka na maganin typhoid in an sha kamar haka. A samo ganyen shuwaka guda 10 zuwa 15 a dafa har sai ruwan ya rage kofi daya sai a bar shi ya yi sanyi sannan a zuba masa zuma a rinka sha a kai a kai kofi daya a kullun.
12.Ciwon Kunne: Shuwaka na maganin ciwon kunne sosai.
Mrs Basakkwace