Home Daga Marubutanmu Idan saɓani ya shiga tsakaninka da mai ɗakinka kuna zama domin tattaunawa...

Idan saɓani ya shiga tsakaninka da mai ɗakinka kuna zama domin tattaunawa kan lamarin komai ƙanƙancinsa?

23
0

Meke kawo rikice rikicen zaman aure a wannan zamanin?

Kashi na farko!

Akwai abubuwa da dama da suke kawo rikice-rikicen zaman aure a wannan zamani da muke ciki. Galibi matsalar ba wai rashin soyayya kaɗai ba ce, har da rashin fahimtar juna da hakkokin juna, rashin haƙuri da sauran abubuwa.

Rashin fahimtar juna;
Wasu ma’aurata ba sa iya fahimtar ra’ayin juna. ba’a girmama ra’ayin juna sam!Ƙaramin abu kan zama babban rikici saboda rashin tattaunawa cikin natsuwa, ko kuma rashin tattaunawa nan take a kan lokaci.
Da ace duk yadda ƴar matsala ƙarama ta kunno za’a zauna a tattauna a samu sulhu da tabbas za’a ji sauƙi a wannan ɓangaren.
Sulhu cikin natsuwa, girmama ra’ayin juna tare saurin ɗaukar laifin da yake naka kan gyara kaso goma daga cikin rikice rikicen zaman aure a wannan zamanin!

Managarciya!

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here