IBB Ya Goyi Biyan Osinbajo Ya Yi Takarar Shugaban Kasa A 2023

IBB Ya Goyi Biyan Osinbajo Ya Yi Takarar Shugaban Kasa A 2023

Tsohon Shugaban kasa Ibrahim Babangida a ranar Alhamis ya fito karara yana goyon bayan takarar mataimakin shugaban kasar Nijeriya Farfesa Yemi Osinbajo a 2023, da yayi takarar shugaban kasa a zabe na gaba.

Janara Babangida ya ce Osinbajo mutum ne na kirki da yake iya jagorantar kasar nan.

Ya fadi hakan ne a lokacin da kungiyar neman goyon baya ta Osinbajo(Osinbajo Grassroots Organization) ta kai masa ziyara a gidansa dake Minna.
Babangida ya nemi mataimakin shugaban kasar ya tsaya domin zai iya jagorantar Nijeriya da kyau.
Ya ce "Nasan Osinbajo sosai mutumin kirki ne da ya damu da kasar nan zai iya biyan muradun mutanen kasar nan, irin wadan nan mutane ake bukatar su jagorancin kasar nan mutumin da ya damu da kasa. Nijeriya kasa ce mai kyau, mutanenta suna da kirki, yakamata ka fahimci mutane kafin ka yi magana kan abin da ya shafe su."