HYPPADEC Zata Horar Da Matasa 5000 A Jahohi Shida Don Samar Ayyukan Yi Na Dogaro Da Kai

HYPPADEC Zata Horar Da Matasa 5000 A Jahohi Shida Don Samar Ayyukan Yi Na Dogaro Da Kai

 

Daga Awwal Umar Kontagora, Abuja

 

Gina matasa ta hanyar samar masu da gurabun ayyukan yi, zai magance matsalar rashin tsaro da samar da kyakkyawar rayuwa ga matasa. Ministan matasa da wasanni, Mista Sunday Dare ne ya bayyana hakan a lokacin da yake waklitar sakataren gwamnatin tarayya, Boss Gida Mustapha a lokacin kaddamar da shirin horar da matasa dubu biyar daga jahohin Neja, da Kwara, Kogi, da Benuwai, jihar Fulato da suke karkashin hukumar raya yankunan da ke samar da wutan lantarki ( HYPPADEC). Ministan ya cigaba da cewar daga cikin kudurin gwamnatin tarayya akwai samar da gurabun ayyuka ga matasa, wanda shirin wannan hukumar yazo daidai da manufar gwamnatin tarayya.

Da yake karin haske, babban darakta mai kula da hukumar, Alhaji Abubakar Sadiq Yelwa ( Katukan Yauri), wace kafin wannan mun kaddamar da shirin tallafawa gundumomi ta hanyar samar da ababen hawa ga jami'an tsaro, bayan nan zamu taba bangaren noma, yau mun kaddamar da shirin horar da matasa maza da mata dubu biyar daga jahohin da aka kafa wannan hukumar domin su.

Saboda bayan horarwa, a karshe za mu samar masu da ababen da suka koya dan tsayuwa da kafarsu, hakan zai taimaka wajen rage radadin aikin yi ga matasa.

Da yake amsa tambayiyon manema labarai, mataimakin gwamnan Neja, Hon. Muhammed Ahmed Ketso, da ya wakilci gwamna Abubakar Sani Bello, yace wannan shiri mai kyau ne, domin al'ummomin da ke zaune a bakin koramun da suke samar da wutan lantarki, da suka hada da Kainji, Shiroro da Zungeru zasu ci moriyar arzikin da gwamnatin tarayya ke samu a yankunan su.

Kamar yadda hukumar ta bayyana a hukumance za ta horar da sana'o'in hannu mabanbanta sama da goma sha biyar, wanda idan an kammala kuma za ta samar wa wadanda suka gajiyar shirin kayan ayyukan da aka horar da su.

Taron dai ya samu halartar wakilan jahohin da abin ya shafa, wanda sarakunan gargajiya ba a bar su a baya ba.