Hukumar Zakka da wakafi ta jihar Sakkwato, ta karbi motoci ukku na daukar maras lafiya a Sakkwato

Hukumar Zakka da wakafi ta jihar Sakkwato, ta karbi motoci ukku na daukar maras lafiya a Sakkwato

 Daga Mukhtar A Haliru Tambuwal Sokoto. 

 

Shugaban Zantarwa Hukumar Zakka da Wakafi ta jihar Sokoto malam Muhammad Lawal Maidoki Sadaukin Sakkwato  ya bayyana cewa Hukumar zakka za ta cigaba da haɗa gwiwa da hukumomi,  ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun jama’a,yan siyasa da sauran duk mai niyar aikin Alkhairin, domin samar da tallafin yin wasu ayyuka na moriyar jama’a.

Shugaban hukumar, ya bayyana haka a yayin da taron kaddamar da wani shirin hadaka na wakafin kiwon Lafiya, mai suna LAHIYA SAK/ SOZECOM Health Waqaf Patnership domin amfanin  al’ummar dan majalisar.
A yayin ƙaddamar da shirin haɗin gwiwar wanda aka gudanar harabar fadar uban kasar, Ɓodinga, shugaban Hukumar SOZECOM, Malam Muhammad Lawal Maidoki, Sadaukin Sakkwato ya sanar da cewa, ɗan majalisar ya ba da motocin ɗaukar marasa lafiya guda uku da za a ajiye ɗaya a kowacce dayan fadar uban kasa,a ƙaramar hukuma da ke yankin mazaɓarsa, don inganta lafiyar al’ummar sa.  Ya ce, an ba da wannan tallafi ne ba tare da la’akari da bambancin siyasa ko wata wariya ba. Shugaban ya bayyana hadaka da irin kokarin da dan majalisar yayiwa Hukumar tun yana kwamishina, yayi kira ga sauran Alummah da suma su shigo su kawo na su tallafin dan inganta rayuwar alummah, ya godewa Dan Majalisar akan wannan aikin da yayi.
A nasa jawabin, Dan Majalisar Hon. Dr. Balarabe Shehu Kakale ya bayyana cewa, wannan tsari wani ɓangare ne na shirin Kiwon Lafiya na Waƙafi, da zai tallafawa mutane dubu huɗu masu buƙatar tallafin lafiya a cikin mazaɓarsa.
Ya buƙaci uwayen kasa da suka fito daga ƙananan hukumomi uku da shirin tallafin ya shafa, su kafa kwamitocin kula da Aikin Kiwon Lafiya na Waƙafi a yankunan su, domin tabbatar da yadda aikin ke tafiya, yayi kira ga kowa da yasaka nashi wakafi cikin Shirin, inda nan take wasu suka bada nasu kudi dan karawa cikin Shirin, Yayi karin haske akan cewa shirin na da  rassa ukku na aikin na Farko na Lafiya Sak, na biyu shirin kaddamar da motocin daukar maras Lafiya guda ukku, inda aka samarwar motocin da direbobi,da mataimakan su, Wayar tafi da gidan ka, Albashin direbobin da mataimakan su, kudin mai da na kira, tare da samar da magunna ga motocin, da biyan duk wani abu da ake bukata har tsawon na shekara daya, domin daukar maras Lafiya, musamman maras hali, Almajirrai,Alarammomi, Mata masu juna biyu, wadan da suka samu hadari, yara da sauran, shi kuma kashi na Ukku kafa Alamomin Hanya, da rage gudu da wayar da kai akan illar tukin Ganganchi da sauran ayukka.
A jawabin sa, Kwamishinan Lafiya na Jihar Sakkwato Dr. Muhammad Ali lnname ya yabawa wannan ɗan majalisa, tare da kira ga sauran ýan siyasa da su riƙa tallafawa ƙoƙarin da gwamnati take yi a harkar lafiya, da kuma tabbatar masa da samun cikakken haɗin kai da goyon bayan gwamnatin jihar.
A saƙon sa na sanya albarka ga wannan aiki,  Sakataren Zartarwar Hukumar Kula da Ilimin Larabci da Addinin Musulunci Dr. Umar Altine Aliyu Dandin-Mahe ya bayyana cewa tsarin Waƙafi, yana samar da cigaban tattalin arziƙi a akasarin ƙasashen Musulmi da ke amfani da wannan tsarin, don haka ya ba da shawarar a yi amfani da shi wajen kula da inganta rayuwar Almajirai da Marayu.
A cikin jawabin su na godiya, Shugaban Ƙaramar Hukumar Boɗinga Alhaji Shehu Muhammad Ɗan Malikin Ɗanchadi, da Uban kasar Boɗinga Alhaji Bello Abdurra’uf,da Shugaban Kwamitin Lafiya Sak,da Jami'in NHIS na yankin Sokoto, sun yi godiya ga Hukumar Zakka da Waƙafi ta jiha, da ɗan majalisar su Dr Balarabe Kakale, bisa wannan tallafi da suka samu.
Kwamishina Lafiya,uban kasar Bodinga, Shugaban Zartarwar Hukumar zakka,Dan majalisar sun kaddamar da motocin tare da baiwa direbon makullayye,wayoyin kira ga direbon tare da kaddamar da duba wasu maras Lafiya da yi masu rijista.