Hukumar zaɓe ta sanya ranar gudanar zaɓen kananan hukumomi a Sakkwato

Hukumar zaɓe ta sanya ranar gudanar zaɓen kananan hukumomi a Sakkwato

Hukumar Zabe mallakar jihar Sakkwato waton SOSIEC ta sanya Assabar 21 ga watan Satumba na 2024 ta zama ranar gudanar da zaben shugabannin ƙananan hukumomi 23 da kansiloli a mazabu 244 na jihar.
Shugaban hukumar Alhaji Aliyu Suleiman a takardar da ya sanyawa hannu ya ce  suna sanar da duk jam'iyyun siyasa da ke da rijista a hukumance su sani za a yi zabe a Assabar 21 ga Watan Satumba.
Suleiman ya kara da cewar tsare-tsare da yanda zaben zai gudana kowace jam'iyar ta je ofishin su domin karbo fom don gani da bin yanda lamarin yake a tsare.