Hukumar Tsaro Ta DSS Ta Yi Kira Ga Jama’a da Su Yi Taka-Tsan-Tsan, Akwai Matsala a Najeriya

Hukumar Tsaro Ta DSS Ta Yi Kira Ga Jama’a da Su Yi Taka-Tsan-Tsan, Akwai Matsala a Najeriya

 

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta bayyana bankado wasu shirye-shirye daga wasu bata-gari da ke son kawo tsaiko da tashin hankali a Najeriya, Punch ta ruwaito. 

Wannan na zuwa ne makwanni biyu da hukumar ta yi gargadin aukuwar barkewar rikicin siyasa a kasar, kamar yadda rahotanni suka bayyana. 
Hukumar ta yi kira ga shugabannin siyasa da masu ruwa da tsaki a fannin da su bi doka da oda ko su tafi kotu idan basu gamsu da wani sashen zabe ba.
A cewar wata sanarwar da hukumar ta fitar ta hannun kakakinta, Peter Afunanya, ta ce yayin da wasu ‘yan siyasa ke neman hakkinsu a kotu, wasu kuwa na tada hankali wajen tofa kalamai masu tada zaune tsaye. 
Sanarwar ta bayyana cewa, barkewar rashin tsaro da za a samu a Najeriya a wannan karon na da alaka da siyasa da kuma masu ruwa da tsaki a fannin. 
Hakazalika, ta ba da shawarin al’umma su kwantar da hankali, inda tace ya kamata ‘yan siyasa su tafi daidai da tsarin dimokradiyya ba ta’addanci ba, rahoton Vanguard.
A bangare guda, kakakin na DSS ya ce, ya kamata jama’a su kula da yadda ake yada labaran karya game da zababben shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu.