How To Make Special Fruit combination

How To Make Special Fruit combination

ZEZA'S CUISINE

Special Fruit combination 

Yadda ake hadawa
 
 
Mangoro ja
Mangoro Kore
Strawberry (faraula)
Apple (tuffa) ja da kore
Abarba
Gwanda
Pear
Sugar syrup (sugar ake narkarwa cikin ruwa a daura kan wuta har sai ya yi kauri)
 

Yadda ake hadawa
 
Da farko za a wanke duk kan kayan marmarinda muka ambata a sama sai ayayyanka su da kyau yadda girman kowani yanka zai zama dai dai.
Bayan angama yankawa sai a kawo narkakkiyar suga a zuba akai a cakude ko ina ya ji, a saka  cikin fridge ya yi sanyi.
 
In ya yi sanyi a dauko a rika ci da cokali ya yin hutawa ko kan a ci abinci ko bayan an ci abinci. 

Ga masu ciwo diabetes za a iya sa musu zuma a maimakon sukari.


Ina son wannan combo yayin da na ke karatu, ina dan duba littafai na, ina kuma cin kayan marmari na. Ya Allah mun gode maka, Allah kar Ka haramta mana cin kayan marmarin  aljanna. Ya Allah muna rokonKa Ka samu aljannarka madaukakiya da rahmarKa ya Arhamarrahimiin .


chief zeza