Home Labarai Hisbah ta kama wata matashiya da ta tsero daga Nijar saboda Auren...

Hisbah ta kama wata matashiya da ta tsero daga Nijar saboda Auren dole

11
0

Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina ta kama wata budurwa ƴar Jamhuriyar Nijar da ta ce ta tsere wa shirin yi mata auren dole a Jibia da ke Jihar Katsina.

Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Jami’in sashen fasahar sadarwar hukumar reshen Jibia, Malam Aliyu Mustapha, ya fitar.

Sanarwar ta ce, jami’an Hisbah sun kama budurwar mai suna Marwanatu Salisu, ƴar Maradi, da misalin ƙarfe 11:00 na daren ranar 23 ga Satumba, 2026, yayin da suke gudanar da sintiri.

Hisbah ta ce, binciken da ta gudanar ya nuna cewa budurwar ta baro Jamhuriyar Nijar ne bayan an shirya yi mata auren da ba ta so,

Sanarwar ta ce, Budurwar ta ce mahaifinta da mahaifiyarta sun rasu kuma tana zaune ne a hannun kishiyar mahaifiyarta.

Hukumar ta ce, ta miƙa budurwar ga Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa a Jibia domin miƙa ta ga jami’an Jamhuriyar Nijar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here