Home Rahoto Hisbah ta haramta kayan See I Love da kiɗan DJ a Sokoto

Hisbah ta haramta kayan See I Love da kiɗan DJ a Sokoto

2
0

Hisbah ta haramta kayan See I Love, wazzigidi, takaita kayan lefe, da wasu bidi’o’i a bukukuwan aure a Sokoto

Hukumar Hisbah ta Jihar Sokoto ta sanar da haramta kayan “See I Love” da wazzigidi ko kuma kide-kide (DJ), saka manyan lasifika a agwagwa da buje (Keke Napep), da kuma wasu al’adun bukukuwan aure.

Da yake jawabi, Kwamandan Hisbah Malam Usman Abdullahi Jatau ya ce dokar ta fara aiki daga ranar 27 ga Yulin 2026, kuma ta haɗa da takaita kayan lefe da sauran al’adun da hukumar ta ce ba su dace da koyarwar addinin Musulunci ba.

Dokar tana da kyau musamman ga mutanen jihar ta Sakkwato ganin yanda ake shan wahala a harkokin aure da sauran bukukuwa.

Amma akwai gyare-gyare da yakamata Hisbah ta yi al’ada ba laifi ba ce matuƙar ba za a saɓawa Allah da ita ba, kayan see I love al’ada ce a jihar da ba za ta kau nan kusa ba, abin da yafi dacewa hukumar ta yi ta gyara ko hana ɓarnar da ta shigo ciki.

Kayan lefe al’ada ce, kayan ɗaki gado da kujeri da kayan amfanin gida duka al’ada ce ɗaya ba zai hanu sai da ɗaya, mafita a ɗaya ce a yi wa’azi mutane su ji tsoron Allah su bar riya, amma hukuma ba za ta iya hana al’adun aure ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here