Hisbah ta fasa kwalaben giya miliyan 3.8 a Kano

Hisbah ta fasa kwalaben giya miliyan 3.8 a Kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta farfasa kwalaben giya iri-iri har miliyan 3.8 da ta kama a ƴan watannin baya a jihar.

Kwamanda-Janar na Hisbah, Dakta Harun Ibn-Sina ne ya baiyana haka yayin fasa kwalaben giyar a ƙauyen Tudun Kalebawa, Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa a jihar.

Ibn-Sina ya ce hukumar na samun nasarar yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi da maye da kuma sauran halayen rashin tarbiyya a jihar.

Ya ce ba a fasa kwalaben giyar ba sai da gwamnatin jihar ta sahale a yi hakan.

Ya ce hakan ne ya baiwa hukumar Hisbah ɗin damar zuwa kotun majistare, wacce ta baiwa hukumar umarnin fasa kwalaben giyar.

Ibn-Sina ya nanata cewa siyarwa da shan kayan maye haramun ne a dokar jihar.

Ya kuma yabawa gwamnatin jihar bisa ƙoƙari wajen yaƙi da matsalolin rashin tarbiyya a jihar, in da ya tabbatar da cewa yanzu haka Kano za ta yi gogayya da kasashen duniya wajen yaƙi da munanan halaye.