Hasashen Yadda Zaben 2023 Zai Kasance Tsakanin APC, PDP, LP da NNPP a Jihohi 36

Hasashen Yadda Zaben 2023 Zai Kasance Tsakanin APC, PDP, LP da NNPP a Jihohi 36


Babu mamaki a zagayen farko a rasa wanda ya yi nasara a tsakanin masu neman kujerar shugabancin Najeriya a zaben shekarar badi. 

Hasashen da This Day ta gudanar, ya nuna cewa ba abin mamaki ba ne sai zaben shugabancin kasa ya kai ga zagaye na biyu tsakanin masu takara. 
Akwai jihohi 21 da ake kyautata zaton Atiku Abubakar mai takara a jam’iyyar PDP zai samu akalla 25% da doka tayi tanadi a zaben shugabancin kasa. 
A gefe guda, ‘dan takaran jam’iyyar APC, Bola Tinubu zai iya tashi da 25% na kuri’u ne a jihohi 20. 
Mr. Peter Obi na jam’iyyar LP ake hangen zai zo na uku a zaben, shi kuma Rabiu Musa Kwankwaso mai takara a jam'iyyar NNPP zai kare a na hudu. 
Jaridar ta fitar da sakamakon hasashen da aka yi a kowane yanki da kowace jihar kasar nan. Hakan ya nuna inda kowace jam’iyya take da karfi. 
A Arewa maso tsakiya, PDP za tayi galaba a Neja, Kogi da Kwara, sai LP ta samu nasara a Filato da Benuwai, sai kuma APC ta karbe Nasarawa. Jam’iyyar APC ake ganin za ta ci Kaduna da yayin da PDP za ta iya nasara a Jigawa, Katsina da Sokoto. Jam’iyyar NNPP kuma za ta karbe Kano. 
Peter Obi da LP ake ganin za su tashi da 60% zuwa 70% na kuri’un Enugu, Ebonyi, Imo, Abia da Anambra. Da kyar sauran jam’iyyu za su tsira a yankin. 
Ana ba Bola Tinubu nasara a Legas, Ogun, Ondo, Ekiti, Oyo da Osun. PDP za ta zo na biyu da 20% a kusan duka jihohin Kudu maso yamma illa Osun. A Arewa maso gabas, an ba APC Borno da Yobe, sai PDP ta lashe 60% na kuri’un Adamawa da rinjaye a sauran jihohin, NNPP za ta ci 5% zuwa 20%. 
A Kudu maso kudu, PDP za ta iya cin Delta, Akwa Ibom da Bayelsa. LP za ta sha gaban kowa a Ribas da Kuros Riba inda Bola Tinubu zai tashi da 25%.