Harin Bam a Sokoto: PDP Ta Jajantawa Iyalai, Ta ba Gwamnati Shawara 

Harin Bam a Sokoto: PDP Ta Jajantawa Iyalai, Ta ba Gwamnati Shawara 


Jam'iyyar PDP ta yi magana kan harin kuskure da sojoji suka kai kan fararen hula a jihar Sokoto. Jam'iyyar PDP ta jajantawa al'ummar jihar Sokoto kan mutanen da suka rasu da waɗanda suka jikkata sakamakon harin na kuskure da aka kai a ƙauyukan Gidan Sama da Rumtuwa.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na ƙasa na PDP, Debo Ologunagba, ya fitar a shafin X a ranar Lahadi. 
Jam'iyyar PDP ta buƙaci a gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da tabbatar da ba da kariya ga fararen hula a yaƙin da ake da ta'addanci a ƙasar nan. "Jam’iyyarmu ta tuna da aukuwar irin wannan lamari da ya yi sanadiyyar salwantar rayukan fararen hula a jihar Kaduna a watan Disamba 2023 da Satumba 2024, tare da yin kira da a ɗauki matakan kaucewa aukuwar irin wannan bala’i a nan gaba." 
PDP ta jajantawa iyalan waɗanda lamarin ya ritsa da su, ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakan da suka dace domin biyan iyalan waɗanda suka mutu diyya, tare da samar da isassar kulawa ga mutanen da suka jikkata. Yayin da ta ke kira da a ƙara sanin makamar aiki, PDP ta buƙaci sojoji da ka da su yi ƙasa a gwiwa a ƙoƙarin da suke yi na yaƙi da ta'addanci a Najeriya.