HANYOYIN 5 DA ZA KU KULA DA KAN KU LOKOCIN HUNTURUN SANYI
Lafiya Uwar Jiki: kula da lafiya abu ne da yake da matukar muhimmanci a rayuwar mutum da jikinsa
1. Sanya kayan sanyi masu nauyi nada matukar muhimmanci a wannan lokacin musamman ma ga yara da kuma tsofaffi domin kare kai.
2. Yana da matukar anfani, mutane su rika saka tubarau da zai rika rufe masu idanuwansu da ma hanci da baki a wasu lokuta domin samun kariya.
3. Yana da kyau mutane su rika shafa mai da ke da maiko sosai a wannan lokacin domin samun laushin fata musamman ma a baki da kuma kafa.
4. Yana da kyau a rika wanke kayan abinci da ganyayyaki da ma 'ya'yan itatuwa sosai kafin ci a wannan lokacin.
5. Haka zalika atisaye da motsa jiki yana da matukar anfani shima domin samun dumamar jiki da kuzari.
Lafiya Uwar Jiki: kula da lafiya abu ne da yake da matukar muhimmanci a rayuwar mutum da jikinsa
managarciya