Hanifa:Da Zaran Kotu Ta Yanke Masa Hukuncin Kisa, Zan Sanya Hannu A Kashe Shi----Ganduje

Hanifa:Da Zaran Kotu Ta Yanke Masa Hukuncin Kisa, Zan Sanya Hannu A Kashe Shi----Ganduje

 

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya yi alkawarin mutunta dokar da kundin tsarin mulki ya tanada a matsayinsa na gwamnan wajen sanya hannu kan hukuncin kisa a irin wannan yanayi, idan kotu ta yanke hukuncin a kan kisan gillar da aka yi wa yarinya ‘yar shekara 5, Hanifa Abubakar.

 

Ya baiyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya tare da mataimakinsa,  Nasiru Yusuf Gawuna, da shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar, Labaran Abdul Madari da sauran manyan jami’an gwamnati, ga iyayen Hanifa da ke Dakata/Kawaji, a jiya Litinin.

 
“Muna da kwakkwaran tabbaci daga kotun da za ta yi shari'ar cewa, za a yi adalci,” in ji shi.
 
Ganduje ya  tabbatar da cewa, “Duk wanda aka samu da wannan danyen aikin, shi ma zai fuskanci kisa ba tare da bata lokaci ba. A matsayinmu na gwamnati mun riga mun fara shirye-shiryen.”
 
Gwamna Ganduje ya ce “Tsarin mulkin mu ya tanadi cewa idan aka yanke hukuncin kisa, ikon da tsarin mulki ya bayar shi ne gwamna ya ba da izinin aiwatar da hukuncin kisan. Ina tabbatar muku da haka, ba zan bata ko da dakika daya ba.”
 
A kan gaggawar gudanar da shari'ar, ya tabbatar da cewa za a gaggauta gudanar da shari'a, inda ya kara da cewa, "gwamnati za ta kula da iyalan marigayiya  'yar mu Hanifa mai albarka."
 
 Makarantun da wannan bala’i ya shafa, Gwamna Ganduje ya bayyana cewa, gwamnati za ta yi wani abu a kan makarantun.
Haka ma gwamnatin Kano ta bayar da sanarwa soke lasisin dukkan makarantu masu zaman kansu a jihar Kano har sai an sake tantance su kamin sake sabunta lasisin na su.
Kwamishinan ilmin jihar ne ya fitar da bayanin ganin wannan lamarin da ya faru dole a zargi akwai wasu bara gurbi da ke tafiyar da harkokin ilmi a Kano.