Halin Da Nijeriya Take Ciki Bola Tinubu Ne Mafi Dacewa Ya Jagorance Ta---Ibrahim Lamido

Halin Da Nijeriya Take Ciki Bola Tinubu Ne Mafi Dacewa Ya Jagorance Ta---Ibrahim Lamido

Dan takarar Sanatan Sakkwato ta Gabas a jam’iyar APC Alhaji Ibrahim Lamido ya bayyana wanda yake ganin ya dace ya jagoranci Nijeriya ganin halin da take ciki na tabarbarewar tsaro da tattalin arziki da rashin aikin yi ga matasa.

Ibrahim Lamido a lokacin da yake managana da manema labarai a filin wasa na Gingiya a Sakkwato  lokacin ziyarar shugaba Buhari da dan takarar shugaban kasa a jam'iyar APC Bola Ahmad Tinubu ya ce Tinubu ne ya dace ya jagoranci kasar nan duba da halin da take ciki a yanzu.

Alhaji Lamido ya ce kasar nan tana bukatar mutum jajirtacce da ke da kwarewa da zai iya saita kasar nan ta fita daga cikin mawuyacin halin da ta samu kanta. 

"Tinubu mutum ne da ya yi an gani ya daura Legos saman turbar cigaba wadda in ya samu nasara a wannan zaben muna sa ran Nijeriya za ta hau saman turba tagari.

"Kwarewarsa a fannin majalisar  dokoki  da zartarwa abu ce da ake so ga duk wanda zai shugabnci kasar don hakan zai sa ba a samu tsaiko ba a lokacin gudanar da muhimman aiyukkan da talaka ke bukata na gaggawa," a cewar Ibrahim Lamido.

Ya nuna gamsuwarsa sosai ga dimbin jama'ar jihar Sakkwato da suka fito tarbar Tinubu kan haka yake da yikinin APC za ta samu nasara a dukkan matakai a jihar Sakkwato, "wannan taron ya kara fito da kashi 80 na al'ummar jihar Sakkwato APC suke marawa baya domin ita ce shugabanni masu son talakawa ke cikinta."

Dan takarar Sanatan ya tabbatar in ya samu nasara al'ummarsa za su samu waklici nagari da zai saurari kukansu ya kuma yi tsaye sai an share masu hawayensu gwargwadon iko.