"Gyaran Targaɗe" Ko ƙara Targaɗe?

"Gyaran Targaɗe" Ko ƙara Targaɗe?
 
Al'ada ce idan mutum ya sami targaɗe a wata gaɓa sai ya tafi wajen "mai gyaran targaɗe".
 
"Gyaran targaɗe" ya haɗa mummurɗawa, lallanƙwasawa, daddannawa da kuma jajjan gaɓar.
 
Babu wani abu wai "gyaran targaɗe" ta wannan siga face ƙara mummunan lahani ga tantani da gaɓar!
 
Da farko, ya kamata a fahimci me ake nufi da targaɗe.
 
Targaɗe yana faruwa ne a gaɓa kawai. 
 
To me yake faruwar a gaɓar?
 
Gaɓa mahaɗa ce da ƙashi da ƙashi suka haɗu. Kuma tantani ne ke riƙe ƙashi da ƙashi a gaɓa. Tantani yana da ɗabi'ar ɗanko, wato yana iya talewa sannan ya dawo yayin motsin gaɓa.
 
Targaɗe na faruwa idan aka samu akasi a wata gaɓa ta murɗe ko ta ɗame ko ta gurɗe ko kuma ta miƙe ko ta lanƙwashe fiye ƙima yayin ayyukan yau da kullum ko kuma yayin wasanni.
 
Idan ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa ya faru, to tantani zai samu lahani ko rauni.
 
Matakan tsananin targaɗe sun haɗa da:
 
Mataki na farko: tantani zai sami ɗamewa ko talewa fiye da ƙima, wani lokacin tare da 'yar yagewa kaɗan!
 
Mataki na biyu: tantani zai yage amma bai kai ga tsinkewa gaba ɗaya ba.
 
Mataki na uku: tantani zai tsinke gaba ɗaya.
 
Mataki na ɗaya da na biyu ana iya jinyarsu a likitancin fisiyo. Amma mataki na uku na iya buƙatar tiyata domin ɗinke tantanin.
 
Saboda haka, idan aka samu targaɗe sannan aka tafi wajen "mai gyara" kuma aka yi irin waɗancan abubuwan da muka ambata a kan gaɓar, to gaskiya ba gyaran targaɗe aka yi ba face ƙara targaɗe.
 
Misali, idan mutum ya sami targaɗe mataki na ɗaya, sannan aka ƙara jajjan gaɓar, to tantani zai ci gaba da yagewa ne, wato daga mataki na ɗaya zai shiga matakin na biyu kenan. Idan kuma a mataki na biyu yake, to zai shiga mataki na uku kenan.