Gwwamnatin Kebbi ta aminta da biyan sama da biliyan daya kudin garatitu da ma'aikatan da suka rasu 445

Gwwamnatin Kebbi ta aminta da biyan sama da biliyan daya kudin garatitu da ma'aikatan da suka rasu 445

Gwamnan jihar Kebbi Dakta Nasir Idris ya aminta da biyan sama da biliyan daya(1,144,428) kudin garatitu da ma'aikatan da suka rasa ransu a lokacin aiki su kimanin mutum 445.
Amincewar ta biyan kudin za ta shafi tsoffin ma'aikatan jiha da ma'aikatan wuccingadi da kananan hukumomi da malaman furamare.
Biyan zai kula daga Disamban 2024 zuwa Maris na 2025 jimlar wadanda za su amfana su ne 445.
Gwamnan ya nuna gwamnatinsa za ta ci gaba da kula walwalar ma'aikata da iyalansu musamman wadan da suka yi wa jiha aiki hakkinsu ba abin wasa ba ne.
Gwamna Idris ya bayyana muhimmancin rike martabar aiki da kyautatawa, gwamnatinsa za ta yi tsayin daka ta ta tabbatar da biyan hakkin ma'aikata a jihar.
Tsoffin ma'aikata a jiha sun kara kira ga Gwamna da ya dore da haka ya biya sauran mutane da ba su fado a tsarin wannan biyan ba,  domin akwai dimbin ma'aikata da suka ajiye aiki da ke jiran hakkinsu daga gwamnati.
Tsoffin ma'aiktan  ba su son a fadi sunayensu sun ce akwai bukatar a duk wata a samu gwamna ya biya irin wadan nan kudade ga wasu mutane in ana yin haka cikin karamin lokaci za a biya kusan kowa ba tare da wani dogon lokaci ba.
Mutanen sun yi kira ga Gwamna Nasir ya dubi tsarin biyan Fansho na jihar domin yi masa gyaran fuska don ya dace da lokacin da ak ciki.
"Da yawan masu karbar Fansho a jihar Kebbi abin tausayi ne kudin da ake ba su ko yini ba za su yi wa mutum a kudin abinci kadai, yakamata a duba lamarin fansho."