Gwamnonin jam'iyar PDP a Nijeriya a yau Laraba a Abuja za su cimma matsaya kan yankunan da za a fitar da shugabannin jam'iya da za su jagaoranci jam'iyar ta adawa.
Daily Trust ta samu bayani maganar karba-karbar tana cikin abin da ya tsayar da kwamitocin mutum 279 da za su gudanar da babban taron kasa na jam'iyar karkashin jagorancin gwamnan Adamawa Umaru Ahmadu Fintiri.
A zaman majalisar zartarwar jam'iyar karo 94 PDP ta kafa kwamitin da zai raba mukaman a kowane yanki na Nijeriya karkashin kulawar Gwamnan Ifeanyi Ugwuanyi kafin babban taron 30 ga Okotoba 2021.
Zaman da kwamitin ya yi a satin da ya gabata a Enugu sun aminta da kudu ce za ta kawo shugaban jam'iya, kwamitin zai yiwa gwamnoni bayanin matsayarsu a yau.
Taron zaman na kungiyar Gwamnonin PDP karkashin jagorancin Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ana sa ran su tattauna wasu muhimman bayanai game da harkar shugabanci.