Gwamnonin PDP Sun Nemi Tambuwal Da Ya Yi Murabus
Sabuwar rigima ta kunno kai in da wasu gwamnoni ciki har da gwamnan Rivers Nyesom Wike suka nemi gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya yi murabus a shugabancin da yake yi masu na shugaban kungiyar gwamnonin PDP.
Wannan buƙatar ta taso ne kan cewa ba su gamsu a ce yana jagorantarsu ba kuma yana neman samun tikitin takarar shugaban ƙasa.
Rabuwar kawunan a tsakanin gwamnonin ta taso ne tun bayan da Tambuwal ya ayyana cewa zai fara tuntuɓa kan tsayawarsa takara a 2023.
Sanarwar da ya bayar ta haifar da cece-ku-ce in aka samu labarin gwamna Wike ya nemi Tambuwal ya ajiye shugabancin ƙunguyar gwamnonin PDP.
Wata majiyar ta shedawa jaridar Vanguard cewa bai yiwu kana ciyaman na gwamnonin PDP kuma kana wani shiri ka zaci ka sha.
Jaridar taso jin ta bakin kwamishinan yaɗa labarai na Rivers amma ba a yi nasara ba.