Gwamnoni 9 Ke Goyon Bayan Atiku Da Wike, Da Wahala Ba Dayansu Ne Zai Yiwa PDP Takara Ba
Wike a halin da ake ciki yana tare da goyon bayan Gwamna biyar daga cikin 13 da jam'iyar ke da su yayin da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya samu goyon bayan hudu.
Gwamna hudu ne ke neman tikitin zama dan takarar shugaban kasa a PDP Su ne gwaman Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da gwaman Bauchi Sanata Bala Muhammad da gwamnan Rivers Wike da gwamnan Akwa Ibom Udom Emanuel.
Gwamnonin da ke goyon Wike su ne Okezie Ikpeazu (Abia); Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu); Seyi Makinde (Oyo); Duoye Diri (Bayelsa) da Samuel Ortom (Benue).
Wadanda ke goyon bayan Atiku Ahmadu Fintiri (Adamawa); Ifeanyi Okowa (Delta); Godwin Obaseki (Edo) da Darius Ishaku (Taraba).
Hakan ke nuna da wahalar gaske ba cikin su biyu ne za a tsayar da daya ba ganin yanda suka samu goyon bayan gwamnoni a jam'iyar
managarciya