Gwamnnatin Tinubu Ta Fadi Lokacin Fara ba Kananan Hukumomi Kudadensu Kai Tsaye 

Gwamnnatin Tinubu Ta Fadi Lokacin Fara ba Kananan Hukumomi Kudadensu Kai Tsaye 

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana lokacin da za a fara ba ƙananan hukumomi kuɗaɗensu kai tsaye. Fadar shugaban ƙasan ta bayyana cewa daga wannan watan na Janairu, ƙananan hukumomi a fadin ƙasar nan, za su fara karɓar kuɗaɗensu kai tsaye daga asusun rarraba kuɗi na tarayya (FAAC). 
Hakan ya fito ne daga bakin mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare, yayin wata hira da ya yi da tashar Arise News. 
Sunday Dare ya tabbatar da ƙudirin Shugaba Bola Tinubu na aiwatar da hukuncin Kotun Koli, wanda aka yanke a watan Yulin 2024, kan ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomi.
Kotun Koli ta yanke cewa ikon da jihohi da suke yi kan kuɗaɗen ƙananan hukumomi ya saɓawa kundin tsarin mulki. Kotun Ƙolin ta yanke hukuncin cewa a riƙa biyan kuɗaɗen ƙananan hukumomi kai tsaye ko kuma ta hannun jihohi.
Sai dai, saboda matsalolin da ake samu idan suka bi ta hannun jihohi, kotun ta umarci a riƙa biyan kuɗaɗen kai tsaye ga ƙananan hukumomi. Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da ministan sharia, Lateef Fagbemi (SAN), ya shigar domin tabbatar da ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomi 774 na Najeriya. Duk da cewa an yanke hukuncin a watan Yuli 2024, aiwatar da shi ya samu jinkiri domin tabbatar da cewa an samar da tsarin da ya dace.