Gwamnatin Tinubu Za Ta Kashe Biliyan 1.37 Kan Wajen Kwanan Ministoci 45 

Gwamnatin Tinubu Za Ta Kashe Biliyan 1.37 Kan Wajen Kwanan Ministoci 45 

 

Jaridar Punch ta rahoto cewa alawus din gidajen sabbin ministoci da aka nada na iya kaiwa naira miliyan 343.25 duk shekara. 

Da wannan kudade da za a ware masu duk shekara, gwamnatin tarayya za ta kashe naira biliyan 1.37 kan wajen kwanan zababbun ministoci 45 cikin shekaru hudu. 
Wannan alawus din ya kasance bisa bayanan da aka tattara daga wata takarda da aka samu a shafin yanar gizo na hukumar tattara kudaden shiga. 
Jerin alawus da ministocin Tinubu za su amfana da shi Wannan ya kunshi alawus din kudin gida (kaso 200 na ainahin albashi) Ma'aikatan gida (kaso 75 na ainahin albashi) Kayan amfanin gida (kaso 30 na ainahin albashi) Kayan daki (kaso 300 na ainahin albashi). 
Sai dai kuma, yayin da za a dunga biyan alawus din duk wata, za a biya na kayan gida sau daya ne a shekaru hudu. 
Ku tuna cewa a kwanan ne shugaban kasar ya sanar da aikin da ya bai wa kowanne daga cikin ministocinsa.