Gwamnatin Tarayya Ta Raba Biliyan 135 Ga Jihohi Don Farfado Da Tattalin Arziki

Gwamnatin Tarayya Ta Raba Biliyan 135 Ga Jihohi Don Farfado Da Tattalin Arziki

 

Gwamnatin tarayya ta raba N135.4bn ga jihohi da kuma birnin Abuja domin farfado da tattalin arziki bayan annobar COVID-19. Rahoton da aka samu daga Punch ya nuna an raba kudin ne bayan lura da yadda jihohi su ka yi kokarin tada komadan tattalin arzikinsu.

Shugaban tsarin NG-CARES, Dr. Abdulkarim Obaje, ya sanar da haka a wani jawabi da ya fitar ta bakin Mr. Suleiman Odapu a ranar Lahadi. 
Suleiman Odapu shi ne jami’in yada labarai da sanarwa a karkashin tsarin na NG-CARES. Bankin duniya ya tallafawa tsarin NG-CARES da $750m da nufin taimakawa kananan ‘yan kasuwa da manoman da COVID-19 ta taba. 
Dr. Abdulkarim Obaje ya ce kudin da aka rabawa jihohin ya danganta ne da kokarin da su ka yi wajen taimakawa wadanda annobar ta shafa. 
Dr. Obaje ya bayyana jihohin da su ka fi yin kokari da kuma adadin kudin da aka ba su. 
Jaridar ta ce jihar Nasarawa ce a kan gaba da ta samu N13.6bn, sai Kuros Riba mai N10.9bn sai kuma jihar Zamfara wanda ta tashi da N10.2bn. 
Wadannan jihohi uku sun tashi da 34,873,631,583.62 daga cikin tallafin biliyoyin da aka raba, ma’ana su kadai sun samu fiye da 25% na kason.