Gwamnatin Tarayya ta Baiwa Gwamnoni Biliyan 30 Don Rage Tsadar Rayuwa Ga Al'umma

Gwamnatin Tarayya ta Baiwa Gwamnoni Biliyan 30 Don Rage Tsadar Rayuwa Ga Al'umma

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Apabio, Ya ce an bai wa gwamnoni Naira Biliyan 30 domin rage radadin tsadar rayuwar da ake fuskanta.

Ya ƙara da cewa baya ga N2bn da gwamnatin tarayya ta ba gwamnoni aro, Ya ce kowace jiha sun samu ƙarin wasu N30bn daga hannun FIRS. 

Kuma ya faɗi haka ne a zaman majalisa na ranar Laraba 21 ga watan Fabrairun 2024, Ya ƙara da faɗin daga wajen kason da gwamnonin suke samu daga asusun tarayya domin a taimaka masu su magance matsalar ƙarancin abinci.

Kazalika, Akpabio ya ce gwamnoni suna da rawa sosai da za su taka, ya nanata zargin cewa suke da iko da ƙananan hukumomin, Kuma ya yi kira ga gwamnatocin jihohi su yi amfani da kuɗin yadda ya dace domin yunwa ta ragu a yankin su.