Gwamnatin Sokoto ta yi magana kan ɓullar cutar Kwalara a jihar

Ma'aikatar lafiya ta jihar Sakkwato ta ce ba wani rahoto da bayyana annobar cutar Kwalara ta ɓulla a jiha.
Babban sakatare a ma'aikatar Alhaji Abubakar Ahmad Walin Gagi ya sanar da hakan ya kuma ce sun ɗauki matakan da ya kamata ko da lamarin ya faru.
Wali Gagi ya shawarci mutane su tabbatar da tsaftar kansu da muhallansu musamman a wannan lokacin na Damana.
Haka ma ya ce akwai bukatar jama'a su tabbata suna shan ruwa masu tsafta.
Ya ce mutane kar su yi wasa ɗaukar matakin kariya ga cutar Kwalara.
Ya yi kira ga jama'a su kawo rahoton duk wata cuta da suka ga ta bayyana a ma'aikatar lafiya ko a wata asibiti don ɗaukar mataki cikin lokaci.