Gwamnatin Sakkwato ta yabawa kokarin kungiyar 'Sokoto Professional Network' kan shirya taron horar da matasa 100 don su san dubarun zamani kan na'ura mai kwakwalwa waton Komfuta, an kammala cikin nasara.
Kwamishina a ma'aikatar bunkasa dubarun zamani na jiha Alhaji Bashir Umar Kwabo ya ce wannan yunkurin ya zo daidai da lokaci kuma zai taimakawa gwamnatin jiha kan kudirinta na samar da sabbin kirkira da bunkasa dubarun zamani.
Kwabo a lokacin da yake kaddamar da taron horon da kungiyar SPN hadin guiwa da Dan Anini Dijital wanda aka yi a dikin taro na Dankkani a satin da ya gabata ya yabawa wanda kirkiri samar da horo ga matasa kan na'uarar Komfuta, ya bayyana wannan hobbasar abar bukata ce daza ta taimaki jiha ga samun cigaban da ake so da gaggawa.
"Hakan ke nuna gwamnati ita kadai ba ta isa ta yi komai in aka hada hannu a wuri daya za a cimma nasarar da ba a yi tunani ba."
Ya karfafa gwamnati a kodayaushe horarwa kan dubarun zamani take baiwa muhimmanci don ganin ta yi nasara a tsarin da ta yi na kawo cigaba wannan yana kunshe cikin matsakaicinbdaftarin da ta samar a tsakanin shekarar 2023 zuwa 2026.
Ya ce ginshikin farko da zai samar da cigaban tsari shi ne samar da horo a dabarun zamani, "Gwamnatin Ahmad Aliyu ta samu nasara matuka in da ta fito da shirin horar da matasa dubu 10 sanin fasahar zamani," ya kara da cewa.
" Abin da shugaban kungiyar ya yi ba zai tafi a banza da wofi ba za a tuna wannan sadaukarwar da jinjina masa a koyaushe."
Da farko shugaban kungiyar Injiniya Zayyanu Tambari Yabo ya ce za su cigaba da fitowa da horarwa ga matasa don su samu cigaban da zai taimaki rayuwarsu.
Horon ya mayar da hankali ne kan sanin Komfuta da abubuwan da ta kunsa bayan kammalawa wadanda suka samu horon zai tamaka musu a harkokin aiki da kasuwanci.
"Mun bayar da horo ga sama da matashi 100 da aka zabo don su amfana da shirin," a cewar Yabo.
Kungiyar 'Sokoto Professional Netwok ta zama wani ginshiki ga samar da cigaban matasa yadda take fito da shiraruwa karfafa matasa.
"In ka duba yanda ake ba su horo su zama masu kwazo a hada su da kayan aiki domin su kawo cigaba," a cewarsa.
Kungiyar ta mayar da hankali kan karfafa matasa ganin an samu cigaba a yanzu da gaba a jiha da kasa baiki daya.
"Muna shiri da tsari da muka fitar duk wanda ya bibiyi shiraruwanmu a shekara buyu zai ga a hankali mun taba kowane bangare na rayuwa kama daga tattalin arziki da bunkasa al'umma, anan gaba kadan za a ga shiraruwa na cigaban mata da kawar da talauci da mutane na musamman da ke bukatar tallafi, za a tabo kowane gefe na jama'a," in ji Zayyanu Yabo.