Home Labarai Gwamnatin Sakkwato ta tura ɗalibbai 22 karatu a Indiya da Pakistan

Gwamnatin Sakkwato ta tura ɗalibbai 22 karatu a Indiya da Pakistan

29
0

Gwamnatin Sakkwato za ta cigaba da ɗaukar ‘yan asalin jiha da suka cancanta domin tafiya karatu a ƙasashen waje.

Mataimakin Gwamna Alhaji Idris Mohammad Gobir ne ya sanar da hakan a lokacin da yake ban kwana sahun farko na ɗalibban da gwamnati ta ɗauki nauyin karatunsu a fannoni da dama don samun ƙwarewa a ƙasar Indiya da Pakistan.

Alhaji Idris Gobir ya ce shirin don ganin an samar ma’aikata a wuraren da suke da ƙaranci, gwamnati tana ɗaukar nauyin karatun kwasa-kwassai da ba a karantar da su Nijeriya.

Mataimakin Gwamna ya nemi waɗanda suka samu damar su 22 da su zama jekadu nagari a ƙasashen da suka samu kansu.

Ya kuma tunatar da su kar su yi wani abu da zai sanya su cikin matsala.

Ya yi kira gare su da su mayar da hankali kan karatun da suka je domin tabbatar da maƙudan kuɗaɗen da aka kashe masu ba su je ga banza ba.

Da farko babban sakatare a hukumar ba da tallafin karatu ta jiha Alhaji Kabir Labaran ya godewa gwamnatin jiha kan ƙoƙarin ta na bunƙasa ilmi a jiha.

Ya ce Gwamnatin Ahmed Aliyu ta biya biliyoyin kuɗi na bashin tallafin karatu da ta gada wurin gwamnatin da ta gabata, in da aka bi su bashi a manyan makarantun Nijeriya da wajenta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here