Home Manyan Labaru Gwamnatin Sakkwato ta nisanta kanta da wani boka da ya baiwa Gwamna...

Gwamnatin Sakkwato ta nisanta kanta da wani boka da ya baiwa Gwamna nasara a zaɓen 2027, ta ba da damar ɗaukar masa mataki

30
0

Gwamnatin APC mai mulkin  Jihar Sakkwato o ta Nisanta Kanta Daga Ayyukan Wani Boka da aka fi sani da  ‘Mai Shaho’ in da ya baiwa Gwamna Ahmad Aliyu nasara a zaɓen 2027.

Gwamnatin APC mai mulki a Jihar Sokoto, ta nisanta kanta kwata-kwata daga ayyukan wani mai sihiri da aka fi sani da suna Mai Shaho, kwanaki kaɗan da ya nuna goyon bayansa ga jam’iyyar.

A wani faifan bidiyo ne da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, wanda ake zargin wannan mai sihiri ne ya fitar da shi, inda aka gan shi yana binne wani Bunsuru(ɗan Akuya) da rai, yana mai cewa ɗan takarar gwamna a  jam’iyyar  ADC Manir Muhammad Ɗan’iya ba zai samu karɓuwa a wajen masu zaɓe ba, don haka zai faɗi zaɓe.

Gwamnatin Jihar Sakkwato na  sanar da  jama’a cewa, ba ta da wata alaƙa ko dangantaka ko kaɗan da wannan mutum ko kuma ayyukansa. Haka kuma, Gwamnati ba ta goyon bayan masu sihiri, ba tare da la’akari da irin jam’iyyar siyasar da suke goyon baya ba.

Haka ma,Gwamnatin Jihar na ƙara sanar da jama’a cewa ba ta da wata alaƙa ko hannu a cikin ayyukan da aka nuna a cikin wannan faifan bidiyo, kuma ba za ta amince da duk wani aiki da ya saɓa wa ƙa’idoji, dokoki da kuma ɗabi’u da kuma tsare-tsaren addini na al’ummar Jihar Sakkwato ba.

 A bayanin da Abubakar Bawa Daraktan Janar, na yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, a Fadar Gwamnatin jihar, ya fitar ya ce  “jihar Sakkwato jiha ce da galibin al’ummarta Musulmai ne, kuma mutanenta suna riƙe da koyarwar Annabi Muhammad (SAW) da Sahabbansa, da kuma bin sawun mujaddadi  Sheikh Usman Dan Fodiyo. Don haka, Gwamnatin Jihar ba za ta amince da duk wani aiki  ya saɓa wa koyarwar Annabi Muhammad S.A.W ba.”

Saboda haka, Gwamnati na kira ga duk wani mutum da ke yin bokanci, dama duk wani da ya kaucewa koyarwar addinin Musulunci dasu ji tsoron Allah su bari, a inda kuma aka umarci Hukumar Hisbah ta Jihar da ta ɗauki matakin da ya dace bisa tanadin doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here