Gwamnatin Neja Ta Umarci Jami'an Tsaro Su Harbe Duk Dan Daban da Aka Gani da Makami 

Gwamnatin Neja Ta Umarci Jami'an Tsaro Su Harbe Duk Dan Daban da Aka Gani da Makami 

Gwamnatin jihar Neja ta umarci jami'an tsaro su harbe duk wani ɗan daba da su ka yi ido huɗu da shi yana ɗauke da mugun makami. An cimma wannan matsayar ce bayan wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a fadar Sarkin Minna, Alhaji Umar Farouk Bahago kamar yadda daily trust ta ruwaito. 
Da yake karin bayani, Shugaban karamar hukumar Chanchaga, Aminu Yakubu Ladan ya ce an ɗauki matakin ne domin bawa mazauna jihar damar gudanar da ayyukansu ba tare da fargaba ba. 
A ƴan kwanakin nan, ana samun karuwar ayyukan daba a Minna, babban birnin jihar Neja. 
An samu rahotannin yadda ƴan dabar su ka kai hare-haren kan masallata yayin gudanar da sallar Tahajjud a watan Ramadan din nan. Ladan ya ce gwamnati ba za ta zuba idanu yara marasa tarbiyya su hana al'umma zaman lafiya ba. 
Musa Adamu Mai Kuɗi Achaza, jami'in hulda da jama'a na masarautar Minna ya tabbatar da amincewa da matakin bawa jami'an tsaro damar harbe duk wanda aka gani ɗauke da mugun makami a jihar Neja.