Gwamnatin Kebbi Ta Mayarda Dukkan 'Yan Gudun Hijira Dake Zuru A Gidajensu Na Asali

Gwamnatin Kebbi Ta Mayarda Dukkan 'Yan Gudun Hijira Dake Zuru A Gidajensu Na Asali

Daga Abbakar Aleeyu Anache.

Shugaban Karamar hukumar mulki ta Zuru da ke jihar kebbi a arewa maso yammacin Najeriya Hon Bala Mohammed Isah Gajere, ya bayyana farin cikinsa bisa yadda zaman lafiya ya samu a wasu yankunan da tashin hankali ya rutsa dasu.

Duk wani dan gudun hijira da ke sansanin yan gudun hijira da ke (DANTUDU GOMO MODEL PRIMARY SCHOOL ZURU) sun koma gidajensu na asali cikin yardar Allah, bayan tattataunawar da aka yi da shugaban karamar hukumar mulki ta Zuru ya tofa albarkacin bakinsa inda ya bayyana cewa Zaman lafiya ya samu a duk inda yan gudun hijira suke 

Hon Bala Gajere ya kara da cewa kamar yadda muka sani wannan gwamnatin tana iyakar kokarinta wajen Inganta harkokin tsaro da lafiyar al'umma tare da hadin kan jama'a domin ganin jami'an tsaro sun samu hadin kan al'umma domin dakile hare-haren'yan tada kayar baya.

Bala Gajere yayi amfani da wannan damar wajen yabawa jami'an tsaro kan marawa gwamnati baya wajen tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da Ingantuwar tsaron dukiyoyi da rayukan al'umma.

Shugaban Karamar hukumar mulki Zuru ya bayyana amincewarsa kan matakin da gwamnatin jihar kebbi da gwamnan jihar kebbi ya bi wajen ganin yan gudun hijira sun koma gidajensu na asali.

Bala Gajere ya yabawa malaman addinai wadanda suka bada rayuwarsu da lokutansun wajen ganin yan gudun hijira sun samu kulawa ta musamman, ya kara da cewa wannan al'amari wanda aka yi cikin lumana kuma da yawun gwamnatin jihar kebbi da amincewar Sanata Abubakar Atiku Bagudu, alama ce ta koyi da salon shugaban kasa Muhammad Buhari.

Yan gudun hijira sun samu isa gidajensu na asali wadanda suka hada da garuruwa kamar haka Kanya Sakaba Dankolo Gilwasa da Danrangi da Gulbin Boka, ta Jihar Neja.

Gwamnatin jihar kebbi tallafawa yan gudun hijira da abinci kudin more rayuwa a matsayin sakayya ga yan gudun hijira bisa gudunmuwar da aka baau wajen tabbatar da jindadi da walwalar su, don susamu saukin rayuwa musamman a wannan yana yi da ake ciki na hare-haren yan bindiga.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar kebbi a karkashin jagorancin Sanata Abubakar Atiku Bagudu zata cigaba da samar da nagartatcen shugabanci tare da lafiya da kowa don samar da karin ayyukan farfado da martabar jihar kebbi.

Rashin tsaro wanda ya kasance daya daga cikin babban kalubalen da gwamnatin jihar kebbi tasa agaba don ganin an shawo karshen wannan matsaloli.

Gajere ya shawarci al'umma kan matsalar tsaro dasu ba jami'an tsaro cikakken goyon baya da hadin kai domin ganin wannan matsala an kai karshen ta.

✍️Abbakar Aleeyu Anache,