Gwamnatin Kebbi Ta Kaddamar Da Motoci 27 Ga Jami'an Tsaro
A wani mataki na karfafa gwiwa Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu ya bayar da Motocin ne ga jami'an tsaro
Gwamnatin Kebbi Ta Kaddamar Da Motoci 27 Ga Jami'an Tsaro
Gwamnan Kebbi Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu ya bai wa jami'an tsaro motoci domin gudanar da aikin sintiri da zai taimaka musu wajen gudanar da ayyukan tsaro a fadin jihar.
A wani mataki na karfafa gwiwa Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu ya bayar da Motocin ne ga jami'an tsaro yayin da ya sanya azamar sake farfado da harkokin tsaron jihar da ya addabi al'umma.
Daga Abbakar Aleeyu Anache
managarciya